Malamin Shi’a ya wanke gwamna El-Rufai kan zargin zagin El-Zakzaky

Malamin Shi’a ya wanke gwamna El-Rufai kan zargin zagin El-Zakzaky

- Wani babban Malamin Shi'a mazaunin garin Kaduna Al Sheikh Muhammad Hamza Lawal yace El-Rufai bai zagi Zakzaky ba

- Yan shi'a sun yi zanga zangar sako malamin su El-Zakzaky a birnin Landan

‘Rashin fahimtar Turanci ne ya sanya yan shi’a zargin El Rufa'i ya kira Zakzaky ‘Dabba’” - Inji Sheikh Hamza Lawal

An bayyana cewar karancin fahimtar harshen turanci ne ya sanya Jama'a musanman mabiya Zazzaky daukar cewa gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa'i ya kira Zakzaky da sunan Dabba.

KU KARANTA: El-Zakzaky: Mabiya addinin shi’a sun yi zanga zanga a birnin Landan

Wani sanannen Malamin Shi'a mazaunin garin Kaduna Al Sheikh Muhammad Hamza Lawal ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a yayin taron Nisfu Sha 'aban da kungiyar, 'yan Shi 'a mai suna Athakalaini ta shirya wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Malamin Shi’a ya wanke gwamna El-Rufai kan zargin zagin El-Zakzaky
Hamza Lawal

Sheikh Hamza Lawal ya cigaba da cewar ga dukkanin masanin harshen turanci ya sani cewa kalmar da El Rufa'i yayi amfani da ita a yayin hirar da akayi dashi, inda yace:

"I know the Animal i deal with " ba tana nufin kiran Mutum Dabba bane, abin nufi shine nasan mutumin da nake takkadama dashi ko alama bata nufin kiran Mutum a matsayin Dabba."

Majiyar Legit.ng tace Sheikh Hamza Lawal ya kara da cewa ya zamo wajibi a gareshi ya fadi gaskiya gami da wayar da kan mabiyan Zakzaky wadanda akafi sani da suna 'yan harka’ ko da wane irin suna zasu kirashi dashi, domin halin da ake ciki maslaha ce ake nema ta musulunci da musulmai bata harka ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wai wani hukunci ya dace da barayin gwamnati?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng