Karya ne! Bani da ko fili a Legas balle in gina hotel inji Yari

Karya ne! Bani da ko fili a Legas balle in gina hotel inji Yari

Jaridun Nijeriya dadama musamman jaridar Sahara Reporters ta wallafo wani labari mai buga zuciya Wanda jaridar ta ce hukamar EFCC ta ce ta bankado wani Hotel da ake ginawa agarin Lagos dake kudancin Nigeria na zunzurutun kudi sama da dalar Amuruka $3m Wanda suka ce mallakar Gwamnan jahar Zamfara ne wato Yari.

Hukumar ta EFCC ta ce an yi amfani da kudaden Paris club ne da gwamnatin tarrayya ta bayar ga jahohin Nigeria domin ayukkan da ba a biyan Albashi amma ankarkatardasu wajen ginin wannan kasaitaccen hotel.

Legit.ng ta samu labarin cewa da yake fitar da martanin a madadin gwamna Yari, jami'in hulda da jama'a na kungiyar gwamnonin Nijeriya Abulrazque Barkindo, ya ce wannan labari ne na neman bata wa gwamnan suna da jami'an hukumar EFCC na jihar Legas suka gaya wa kafafen labaru cewa gwamnan ya mallali hotel din da darajarsa ta kai ta dalar Amuruka miliyan 3 wanda ya gina a cikin Legas da kudin da aka rabawa jihohi na Landon Paris domin biyan hakkokan ma'ailatan jihar.

Karya ne! Bani da ko fili a Legas balle in gina hotel inji Yari
Karya ne! Bani da ko fili a Legas balle in gina hotel inji Yari

KU KARANTA: Buhari ya amshi aikin wasu tituna

Ya ce wannan labarin karya ce tsagwaronta domin Yari bai da ko fegi balle gina wani katafaren gida a cikinta.

Sannan ya ja kunnen hukumar da ta daina amfani da kafafen sadarwa wajen fallasa bayanan da basu da tushe balle makama, har sai an kai kotu ta tabbatar da laifin wanda ake zargi, ya kuma zargi cewa irin wadannan bayanan karyar da suke samu shi ke sa ko sun je kotu ake tika su da kasa kamar yadda hakan ta faru da su a kararrakin da ake yi da su.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel