To fa! Ragon suna na shirin raba aure a Sakkwato

To fa! Ragon suna na shirin raba aure a Sakkwato

- Wata mata a unguwar Alkammawa a karamar hukumar Sakkwato ta Arewa ta dankara mai gidanta a kotun shari’ar musulunci akan zargin kin yanka wa ‘ya’yan su biyu ragon suna.

- Ta ce ba abunda mai gidan nata ya yi a lokacin da ta haifi ‘yayan Idris da Khadija masu shekaru 3 da watanni biyar, illa ya sanya masu suna.

Matar mai suna Rukayya Hamza ta kuma ce mijin ba ya ciyar da ita kuma ya na lakada mata duka.

Legit.ng ta samu labarin a don haka ne ta roki shugaban kotun Faruk Ibrahim da ya warware auren ta da mijin mai suna Gazali Garba.

Mijin ya amsa cewa bai yanka wa ‘yayan nasa ragon suna ba, amma ya musanta sauran laifukan.

To fa! Ragon suna na shirin raba aure a Sakkwato
To fa! Ragon suna na shirin raba aure a Sakkwato

KU KARANTA: Cin hanci: An fara shari'a da tsohon shugaban kasa

Ya fada wa kotun cewa bai hana matar ci ba kuma bai da ke ta ba kamar yadda ta fada.

Ya ce a duk lokacin da matar ta haihu ba shi da kudi, shi yasa bai yanka wa yaran ragon suna ba.

Kotun ta bukaci matar da ta gabatar da shaidu akan laifukan da ta zargi mijin.

An daga sauraran karar zuwa ranar 23 ga watan Mayu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel