Wasu daga cikin yan matan Chibok na bukatan aikin Tiyata – Minista Jummai Alhassan
Sakamakon gwajin da akayi kan yan matan Chibok 82 da Boko Haram ta sako ya nuna cewa wasu daga cikinsu na bukatan aikin tiyata, inji ministan harkokin mata, Aisha Jummai Alhassan.
Ministan ta bayyana wannan ne a wata hira da yan jarida ranan Alhamis a Abuja kwanaki biyar bayan an saki yan matan.
Aisha tace. “ A yanzu haka yan mata Chibok 82 na cikin gwaji a Abuja. Wasu daga cikinsu na bukatan aikin tiyata….. za’a karashe wannan cikin makonni 2 zuwa 3.”
Ministan ta musanta maganar cewa gwamnatin tarayya ta hana iyaye ganin yaransu da aka sake har da 21 da aka sako a watan oktoban 2016.
KU KARANTA: An damke wana ya sassari kaninsa
Tace an tura hotunan mata 82 zuwaga iyayensu ranan asabar kuma an bari wadanda aka sako tun da su hadu da iyayensu.
“Mun gana da iyayen yan mata 21 kuma iyayen da yaran sun amince da cewa gwamnatin tarayya ta turau karatu. Yawancinsu na tsoron komawa Chibok,”
https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng