Babbar magana! Wata kyakkyawar dalibar makarantar sakandare ta bace a Jigawa

Babbar magana! Wata kyakkyawar dalibar makarantar sakandare ta bace a Jigawa

- Gwamnatin jihar Jigawa gwamnati ta ayyana bacewan wata daliban makarantar sakanadare mai suna Rukayya Sani, bayan ta tsere daga makaranta don malamin ya mata alkwarin zai mata bulala 20 a kullun har na tsawon kwanaki 5.

- An ce Malamin ya riga ya mata bulala 20 kafin ya mata alkawarin zai mata irin haka a kullun a sauran makon.

Rukayya Sani, daliban makarantan kwana ne na Junior Girls Science School da ke karamar hukumar Miga, an sanar da rahoton bacewan ta bayan ta tsallake katangar makarantan domin ta guje ma hukuncin malamin ta.

Legit.ng ta samu labarin kafafen yada labarai ta Aminiya wato Daily Trust ta ce ta samu labarin cewa an malamin ya hukunta daliban ne akan wani labarin da yarinyan ke yadawa a makarantan mai cewa mallamin na soyayya da daya daga cikin daliban na shi.

Babbar magana! Wata kyakkyawar dalibar makarantar sakandare ta bace a Jigawa
Babbar magana! Wata kyakkyawar dalibar makarantar sakandare ta bace a Jigawa

KU KARANTA: Yar Najeriya mai shekara 63 ta haihu

An tuntube Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar Jigawa, Hajiya Rabi Ishaq, inda ta ke cewa a yanzu haka ‘yan sanda sun riga da sun kama shi wannan malamin.

Ta kuma kara cewa an riga an kafa wani kwamiti da zata don neman ita wannan daliban, karawa da cewa, gwamnatin jihar na aiki da ‘yan sanda da ma’aikatan hanya da hakimin garin Miga da shi kuma malamin da ‘yan sanda suka kama, da iyayen yarinyan da sauran mutanin da ya kamata wajen neman ita wannan yarinyan.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: