Maganar karin albashin Ma’aikata tayi karfi
– Ma’aikata na neman karin albashi a Najeriya
– Yanzu haka dai maganar ta kara nisa
– Bukola Saraki da Yakubu Dogara sun zauna da Ministan kudi
Shugabannin Majalisa sun zauna da Ministan kudin Najeriya.
Saraki da Dogara sun tattauna da Minista Kemi Adeosun.
Minista Chris Ngige da Shugaban Kungiyar kwadago Ayuba Wabba ya halarcin taron.
Tun ba yau Kungiyar Kwadago ta Kasa ta nemi Shugaban Kasa ya kara albashin ma’aikatan Najeriya. Watakila wannan Gwamnatin ta kara albashin ma’aikatan don da alamu yanzu maganar tayi karfi.
KU KARANTA: Ka ji wani shiri na Gwamnatin Tarayya
An yi wannan taro ne a ofishin shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki inda Ministar kudi Kemi Adeosun da Chris Ngige da kuma shugaban kwadago na kasa Ayuba Wabba ya halarta yace su na neman karin kudi zuwa N56,000 kuma magana na tafiya.
Tun kwanaki Ayuba Wabba, Shugaban wani bangare na Kungiyar NLC yace sun gabatar da rokon su ga Shugaba Buhari, ana kuma sa ran ya duba wannan batu. Kungiyar Kwadago na kokarin ganin an maida albashin ma’aikata ya kai akalla N56000 a kowane wata.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wa za ka zaba tsakanin Fayose da Buhari
Asali: Legit.ng