Jay Jay Okocha na Najeriya ne gwani na-Inji Ronaldinho
– Tsohon Tauraron Duniya Ronaldinho yace shagon sa shi ne Okocha na Najeriya
– Ronaldinho yace ba a taba lamba 10 da ya burge sa irin Okocha ba
– ‘Yan wasan sun taka leda tare a Kungiyar PSG.
Dan wasan kasar Brazil Ronaldinho yace Okocha ne shagon sa a kwallo.
Tsohon Dan wasan na Barcelona in dai lamba 10 ake magana sai Okocha
Ronaldinho ya zama gwarzon Duniya har sau 2 a jere.
Tsohon Dan wasan Duniya na kasar Brazil Ronaldinho yace tun da yake kwallo bai taba ganin ‘Dan wasan da ya burge sa ba irin Austin Jay-Jay Okocha na Najeriya. Ronaldinho sun hadu ne da Okocha kwanan nan a kasar Bahrain.
KU KARANTA: FIFA za ta binciki ciniki Pogba
Manyan ‘Yan wasan sun buga wasa tare a Kungiyar PSG ta kasar Faransa kuma ba mamaki Ronaldinho ya koyi darasi wurin tsohon Kyaftin din na Najeriya. Ronaldinho ya saka wani hoto da suka dauka tare a shafin san a Instagram.
Duk da Real Madrid ta sha kashi a hannun makwabtan ta Atletico Madrid ta isa wasan karshe. Watakila Real Madrid din tayi abin da ba a taba yi ba bana idan ta kara Juventus an yi mai-man abin da ya faru a shekarar 98.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Dubi abin da wata Budurwa ke yi
Asali: Legit.ng