‘Yan sanda sun cafke wani mutum da ya kashe karamin yaro don magani

‘Yan sanda sun cafke wani mutum da ya kashe karamin yaro don magani

- Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta kama wani mutum bayan da ya kashe wani dan kaninsa mai kimanin shekaru 4 da haihuwa don maganin kudi

- Hukumar ta ce zata ci gaba da binciken wannan dan talikin

Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta kama wani mutum da ya kashe wani yaro karami ya kuma sara shi gunduwa –gunduwa.

Shi dai mutumin da aka kama mai suna Abubakar Abdulkadir, mai kimanin shekaru 50 da haihuwa da aka fi sani da Sambo, mazaunin kauyen Alin Gora ne dake cikin karamar hukumar Ardo Kola, dubunsa ta cika ne bayan da ya kashe wani dan kaninsa mai kimanin shekaru 4 da haihuwa, ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa kafin daga bisani ya dafa wani sassan jikin yaron.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Mista Yakubu Yunana Babas, wanda shine kwamishinan yan sandan jihar Taraba, ya tabbatar da kama wannan mutum, ya kuma ce zasu ci gaba da binciken wannan dan taliki.

‘Yan sanda sun cafke wani mutum da ya kashe karamin yaro don magani
Malam Abubakar Abdulkadir wanda ya kashe dan kaninsa don maganin kudi

To sai dai kuma da yake amsa tambayoyin manema labarai, Abubakar Abdulkadir, ya ce ya dafa naman yaron nema domin yin magani.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta umarci a ɗaure mata tsohon minista Bala Muhammed a gidan yari

Haka kuma rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta samu nasarar bankado wata maboyar bata gari da suka hada da masu garkuwa da mutane da kuma yan fashi da makamin dake addabar jama’a a jihar, kamar yadda kwamishinan yan sandan jihar ya tabbatar.

Jihar Taraba dai na cikin jihohin dake fama da matsalar masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, batun da kwamishinan yan sandan ke cewa suna samun nasara a yanzu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: