Yan Najeriya ba zamu samu labarin Buhari daga bakinmu ba – Garba Shehu
-Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, yayi hira da yan jarida
-Yace bai tunanin zai je Landan duba shugaba Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya koma birnin Landan ranan Lahadi, 7 ga watan Mayu domin jinyarsa amma bai bayar a takamamman ranan da zai dawo ba.
Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya bayyana cewa su kansu makusantan Buhari sai dais u samu labari daga masu jinyan shi.
Legit.ng ta bada rahoton cewa shugaban kasa ya tafi Landan domin ganin likita kamar yadda ya bayyanawa yan Najeriya kafin yanzu.
Garba Shehu wanda yayi wannan bayani a wata hiran tashar Channels Tv yace ba zai je Landan domin ganin shugaban kasa ba amma wadanda ke tare da shi zasu dinga basu labarin abinda ke faruwa.
KU KARANTA: Manufarmu daya da shugaba Buhari - Amurka
“Ba tunanin zan je, ina tunanin shugaban kasan na bukatan zama da likitocina har ya samu lafiya.”
Kafin yanzu, shugaba Buhari yayi kwanaki a Landan kafin ya dawo ranan 10 ga watan Maris, 2017.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng