Yadda Aku ya fallasa mua’malar Magidanci da ýar-aiki ga Uwargida

Yadda Aku ya fallasa mua’malar Magidanci da ýar-aiki ga Uwargida

-Tsuntsu Aku ya fallasa soyayyar maigidansa da yar-aiki ga Uwargijiyarsa

-Ana samun yawan matsaloli tsakanin ma'aurata musamman a gidajen da akwai Aku

Da alamu hatta dabbobi na jin haushin irin dabbancin da wasu magidanta suke aikatawa da masu aikinsu a bayan idon matayensu, a haka ne wani Aku ya fallasa asirin maigidansa, da hakan ya kusan aikawa da shi kurkuku.

Shi dai wannan Aku ya tona asirin maigidan nasa ne ta hanyar maimaita kalaman batsa da yaji Maigidan na furta ma yar aikin tasu idan Uwargidar bata nan, dama dai tun tuni Uwargidar ke zargin akwai wani alaka tsakanin yar aikinsu da maigidanta, inji rahoton Al-Shahed na kasar Kuwait.

KU KARANTA: Jami’an hukumar hana fasa-ƙauri sun yi harbe harbe da masu fasa-ƙauri a Ogun

Da takaddama ta kaure, sai Uwargida tazo ta dauki Aku ta kai shi ofishin yansanda don ya zame mata shaida, don a hukunta mijin nata, dayake a kasar Kuwait, hukuncin zina shine zaman gidan kurkuku ko kuma horo mai tsanani.

Yadda Aku ya fallasa mua’malar Magidanci da ýar-aiki ga Uwargida
Aku na kallo

Sai dai kash! Allah ya tarfa ma garin mijin nata nono, yayin da hukuma tace ai ba za’a iya amfani da wannan a matsayin hujja ba, tunda babu tabbacin a bakin mijin shi Akun yaji wannan kalamai, zai iya yiwuwa a Talabijin yaji ko a rediyo.

Legit.ng ta samo bayanai dake bayyana Aku a matsayin wata dabba data dade tana hada rikici tsakanin ma’aurata da masoya, haka ma a shekarar 2006 wani Aku ya lalata soyayyar uwardakinsa Suzy da saurayinta Chris, a lokacin daya kwala ihu ‘Ina sonka Gray’, wato sunan wani saurayinta na daban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda ake tsimin albashi a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng