Lallai! Anyi ram da sojan karya (Hotuna)
- Anyi ram da wani dan kasuwa mai karyan cewa shi soja ne
- An damke shi ne bayan ya hallaka wani direban tanka a Abeokuta
- An damke shi da bindiga, kayan soji da lamban mota daban-daban
An damke wani mutum mai suna Tunde Olatunbosun, wanda ke karyan cewa hi soja ne kan laifin kisan wani direban tanka a Abeokuta.
Hukumar yan sandan jihar Ogun ta damke shi ne da bindiga, kayan soji da lambobin motoci daban-daban.
Olatunbosun ya bayyana cewa lallai ya aikata laifin lokacin da aka kama shi tare da wasu abokansa ranan Litinin,8 ga watan Mayu.
KU KARANTA:
Daga baya yace ba da gangan ya kashe direban tankan ba.
An damke shi kwana 2 bayan ya hallaka direban mai suna Rasaq, a Leme a Abeokuta.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng