Gwamna Ganduje ya kai wa mahaifin sanata Kwankwaso ziyara (Hotuna)
- Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci mahaifiyar sanata Musa Kwankwaso a fadarsa da ke garin Madobi
- Gwamnan ya yi wannan ziyara ne bayan ta’aziyar mahaifiyar shugaban karamar hukumar Madobi
Mai Girma Gwamna jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyara wajen Hakimin Madobi kuma Majidadin Kano Alhaji Musa Kwankwaso a fadar sa dake garin Madobi.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, gwamna Ganduje ya je garin Madobi ne domin ta'aziyar rasuwar mahaifiyar shugaban karamar hukumar Madobi.
KU KARANTA KUMA: Gwamnonin APC na yunkurin daukar nauyin musanyar sabon dan takarar jam'iyyar don takarar 2019.
Za a iya tunawa dai cewa gwamna Ganduje ya kasance mataimakin Rabiu Kwankwaso a lokacin da yake gwamnan jihar, amma jim kadan bayan rantsar da Ganduje a matsayin gwamna sai rashin jituwa ya shiga tsakanin shugaban biyu.
Har yanzu dai samman doya da manja suke yi da juna, inda rahotannin baya-baya nan ke nuna cewa tsohon gwamnan na shirin sheka daga jam’iyyar mai mulki APC zuwa PDP.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ku kali yadda gwamnan jihar Ogun ke tukar uwargidansa
Asali: Legit.ng