Ka ji irin ribar da Kamfanin simintin Dangote ta samu a bara
– Alhaji Aliko Dangote bai san da matsin tattalin arziki a Najeriya ba
– Kamfanin simintin Dangote ya samu riba a shekarar bara
– Kamfanin siminiti Dangote yayi kaurin suna a Afrika
Duk da ana fama da durkushewar tattalin arziki Dangote bai durkushe ba.
Asali ma wata kazamar riba ya samu a kamfanin sa.
Sanannen abu ne cewa duk Nahiyar Afrika Dangote bai da sa’a.
Dangote mai kudin Najeriya da ma Afrika gaba daya bai san da cewa ana fama da matsin tattali a Najeriya ba don kuwa ribar sa kurum yake cigaba da samu babu kama hannun yaro. Dangote ya samu bunkasar fiye da rubu’in uwar kudin sa a kamfanin siminti.
KU KARANTA: Shugaban kasa ya san da batun kudin Ikoyi
A dalilin irin ribar da Dangote ya samu kamar yadda Legit.ng ke samun labari zai raba siminti mota guda mai cin buhuna 600. A bara dai Kamfanin Dangote ya samu ribar kashi 25% inda ya tabbatar da matsayin sa na jagoran masu siminti a kaf Afrika.
Kuna da labari cewa Alhaji Aliko Dangote ya samu wata riba a wajen harkar sukari a shekarar bara na sama da Naira Biliyan 14 idan ma an cire haraji da sauran hakkoki kenan.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wani Babban mawaki Najeriya Iyanya
Asali: Legit.ng