Kungiyar Miyetti Allah tayi tir da dokar hana kiwo na gwamnatin Jihar Binuwai
- Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da majalisar dokokin jihar Binuwai don hana makiyaya kiwo
- Shugaban kungiyar ya ce dokar hana kiwo na gwamnatin a maimakon gyara hakkan zai kawo mummunar barna ne
- Shugaban ya yi kira da baban murya ga duk hukumar da ta dace da ta ja hankalin gwamnatin jihar Binuwai da gaggawa
Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta nuna rashin amincewa da dokar da majalisar dokokin jihar Binuwai, a arewa ta tsakiyar Najeriya, ta kaddamar da hana makiyaya kiwo a dazuzzukar jihar in banda kebatattun filaye da masu kiwo suka mallaka.
Sakataren kungiyar Baba Ganjarma, ya shedawa manema labarai a Abuja cewa dokar zata yi karan tsaye ga lamuran kiwo da zaman tare a yankin.
Ganjarma ya kara da cewa dokar zata datse burtalin shanu da ya ratsa ta jihar ta inda Makiyaya ke bi su tafi kudancin Najeriya.
Sakataren kungiyar ya kara da cewa dokar ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ya kawowa kungiyar damuwa saboda haka kungiyar zata dauki duk matakin da doka ta tanada ganin cewa wannan doka bata yi aiki ba.
KU KARANTA KUMA: An yanke hukunci zaman kurkukun shekara 7 ga mutumin yayiwa yar shekara 12 fyade
Yana mai cewa dokan kanta tayi karo da tsarin mulki na tarayya wanda ya baiwa kowane dan kasa ya tafi ya kuma zauna a koina a tarayyar Najeriya, ba tare da tsangwama ba.
Baba Ganjarma, ya yi kira ga duk hukumar da ta dace da ta ja hankalin gwamnatin jihar Binuwai, akan wannan doka da ta aiwatar domin magance shi cikin gaggawa shine zai kawo kyakkyawan fahimta.
Kungiyar ta yabawa jihar Bayelsa, da ta ware kadada 1,200 domin makiyaya da nuna takaicin yadda jihar Binuwai dake tsakiyar makiyaya wanda yake tarihin huldan Tivi da Fulani, amma majalisar dokokin jihar ta kafa dokar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon rikicin kudancin Kaduna
Asali: Legit.ng