Ta-zo-mu-ji-ta: Karya 3 da aka saba yadawa a Najeriya

Ta-zo-mu-ji-ta: Karya 3 da aka saba yadawa a Najeriya

– Wani Farfesa a Amurka ya jero wasu karya da aka saba fada a Najeriya

– Da yawa har su na ganin cewa hakan gaskiya ne

– Wannan na bayuwa zuwa ga yawan maimata labarin

Farfesa Farouk Kperogi da ke can kasar Amurka ya kawo wasu shafa labari shuni da aka saba fada a Najeriya.

Wasu dai har su na dauka cewa maganar gaskiya ce.

Daga ciki akwai irin maganganun da ake alakantawa da Robert Mugabe na Zimbabwe.

Ta-zo-mu-ji-ta: Karya 3 da aka saba yadawa a Najeriya
Farouk Kperogi masanin harshen turanci

Wani Farfesan Turanci a kasar Amurka ya kawo wasu ta-zo-mu-ji-ta da aka saba yadawa a kasar nan kamar da gaske. Kadan daga cikin su wanda ba wai daga bakin Farfesan ba:

1. Wole Soyinka bai da kokari a Makaranta

Za ka rika ganin jin labarai na yawo cewa Farfesa Wole Soyinka ko wanin sa ya kammala Jami’a ne da mataki na 3rd class saboda rashin kokarin sa daga baya kuma ya zama Farfesan Duniya.

KU KARANTA: Ya kamata Arewa ta dana mulki yanzu-Okupe

2. Kalaman Mugabe

Ba mamaki ka saba ganin kalamai da dama ace shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ne ya fade su wanda kusan duka tatsuniya ce da Jama’a su ka kirkiro kamar yadda ake yi da tsohon shugaba Babangida da Obasanjo a kafafen zamani.

3. Kataborar Donald Trump

Ka sha jin cewa Donald Trump ya saba zagin Najeriya da Afrika sai dai bai taba yin wannan katobara ko sau daya ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asalin Dan Najeriya ya zama Dan damben Duniya

Asali: Legit.ng

Online view pixel