Daya daga cikin shayarin marigayi Umaru Musa Yar'adua, ku karanta....

Daya daga cikin shayarin marigayi Umaru Musa Yar'adua, ku karanta....

- Yau ne rasuwar tsohon shugaban kasa Alhaji Umaru Musa 'Yar'Adua ta cika shekaru 7 dai-dai

- An haifi marigayi 'Yar'Adua a ranar 16 ga watan Agusta 1951, kuma Allah ya yi masa cikawa a ranar 5 ga watan Mayu 2010

A yau Juma'a ne ta yi daidai da cika shekaru 7 da rasuwar Matawallen Katsina kuma tsohon shugaban kasa,wato malam Umaru Musa 'Yar'Adua. Ya rasu ne a ranar 5 ga watan Mayu 2010.

An haifi marigayi 'Yar'Adua a ranar 16 ga watan Agusta 1951 kuma ya kasance shugaban Najeriya na biyu a Jamhuriyar ta hudu.

Legit.ng ta kawo daya daga cikin shayarin marigayi Umaru Musa Yar'adua:

"Ni mutum ne kamar kowa, bani da bambanci da talaka ko mai kudi, cuta kuma daga Allah take, shi ke kashewa kuma shi ke rayawa, zan iya mutuwa kuma zan iya rayuwa, zan iya mutuwa yau, zan iya mutuwa gobe, zan iya mutuwa mako mai zuwa, zan iya mutuwa wata me zuwa ko shekara me zuwa, kuma watakila zan iya rayuwa har tsawon shekaru 90 Allah ne kadai masani".

Tunawa da tsohon shugaban kasa marigayi Alhaji Umaru Musa Yaradua (Hotuna)
Tsohon shugaban kasa Alhaji Umaru Musa 'Yar'Adua

KU KARANTA KUMA: Sarkin musulmi ya gargadi ‘yan Najeria

Da fatan 'yan siyasar mu zasu rika yin koyi da irin kyawawan dabi'u da siyasa irin na marigayi 'Yar'adua.

Tunawa da tsohon shugaban kasa marigayi Alhaji Umaru Musa Yaradua (Hotuna)
Tsohon shugaban kasa marigayi Alhaji Umaru Musa Yaradua a lokacin da yake sallah a idi

Allah ya jikansa, yasa aljanna ce makomar, Amin!

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon direban Bishof David Abioye wanda ya karbi musulunci yayin da ya yi murabus da cocin Living Faith Church

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: