Za’a ci tarar duk wanda ya ci mutuncin tutar Najeriya maƙudan kuɗi, Karanta

Za’a ci tarar duk wanda ya ci mutuncin tutar Najeriya maƙudan kuɗi, Karanta

-Majalisar wakilan kasar nan ta ga dacewar a yi doka don kare martabar tutar Najeriya

-Majalisar ta kawo kudirin doka da zata hukunta duk wanda ya ci mutuncin tutar Najeriya

Wani kudirin doka daya tanadi biyan tar na N100,000 ga duk wanda ya keta haddin tutar Najeriya ya tsallake karatu na biyu a bainar majalisa a ranar Alhamis, 4 ga watan Mayu.

Da majalisa daya kawo wannan kudiri, Sam Onuigbo yace manufar dokar itace dawo da martabar da Najeriya da tutar ta, jamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: ‘Kada kayi ƙasa a gwiwa’: Maitama Sule ya shawarci Buhari akan yaƙi da ɓarayi

Sam yace sau dayawa zaka ga ana zane zane akan tutar Najeriya, musamman gwamnoni da wasu yan majalisu, har ma da mutane masu zaman kansu, inda dan majalisan yace wannan cin mutuncin tutar Najeriya ne.

Za’a ci tarar duk wanda ya ci mutuncin tutar Najeriya maƙudan kuɗi, Karanta
Tutar Najeriya

Sam yace bai kamata wani ya lalata tsarin tutar Najeriya kamar yadda Michael Akinkunmi ya tsara shi ba a shekarar 1959, don haka ne ya bukaci a tanadi horo mai tsanani ga duk wanda ya keta haddin tutar, inda ya bukaci a sauya tarar N100 da ake biya a baya, zuwa N100,000.

Za’a ci tarar duk wanda ya ci mutuncin tutar Najeriya maƙudan kuɗi, Karanta
Majalisar wakilai

Sauran yan majalisu sun nuna bacin ransu ga yadda jami’an gwamnati ke lalata tutar Najeriya, haka zalika majiyar Legit.ng ta ruwaito wani dan majalisa daga jihar Ribas yana shawartar gwamnati data wayar da kan jama’a akan mutuncin tutar Najeriya ga kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Menene ra'ayin jama'a?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng