Shin ko kun san, yawan gishiri a abinci yafi komai hatsarin kawo hawan jini?

Shin ko kun san, yawan gishiri a abinci yafi komai hatsarin kawo hawan jini?

- Gishiri in ba kai ba miya, Gishiri sinadarin girki

- Masana kiwon lafia sun tabbatar cewa rashin gishiri a jiki yana kawo cutar goitre, wata cuta mai kumbura maqoqon wuya har ya girma kamar gwanda

- Haka kuma yawan gishirin a jiki yana kawo hawan jini, sakamakon kaurara jini da yake yi har zuciya ta gagara buga shi cikin sauki

Kowacce dabba tana buqatar gishiri, ko a abinci ko a abinsha, sukan lasa ko su sha, amma bil adama ya fi buqatar gishiri nau'in NaCl wanda a bokonce ake ce masa sodium chloride.

Shi dai wannan sinadari ana samunsa a teku, inda yake haduwa ya taru, sakamakon turarewar ruwan da ya tara shi zuwa gajimare. Shi gishirin sai ya kwanta a qasa fari fat, kamar yadda ruwan sama ya wanko shi a lokacin yana cikin duwatsu da qasa.

Ana zuba shi a girki dai dai misali, amma yawaitar kayan zaqaqa miya irin su kafi-zabo, maggi da dunkule na sauran nau'uka, yasa masu harkar kichin kan zuba gishiri cikin girki har yayi yawa. Su dai sinadaran gyara girki na zamani, da gishirin a cikinsu, amma mutane ba lallai sun kula ba, sai su zuba gishiri kamar yadda suka saba, miya tayi jau!

A bincike da masana suka gano, shi wannan yawan gishiri a abinci yana shiga jiki ya illata mutum, inda yakan saka ma jini kauri da jan ruwa fiye da kima. Ita kuwa zuciya, wadda aikin ta daya tilo shine buga jini zuwa sauran sassan jiki, takan takura in jinin nan yayi kauri, har takan gagara aiki daidai, wanda hakan ke saka ta yin aiki da qarfin tsiya, ta harba jini da qarfi, wanda ke zamowa cutar hawan jini, wato High Blood Pressure a turance.

Mata masu iyali, sai a kula da yawan gishiri a miya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel