An rabawa Amare 700 sandunan dukan mazajensu, idan sun bugu da giya

An rabawa Amare 700 sandunan dukan mazajensu, idan sun bugu da giya

-Gwamnatin kasar India ta fito da wata hanyar magance cin zarafin mata

-Gwamnatin ta raba ma amare sandunan dukan namiji idan ya dawo gida a buge

A cikin kayan gara da Gwamnatin kasar Indiya ta yi wa wasu Amare 700 da ta dauki nauyin aurar da su a jihar Madya Pradesh, gwamnati ta baiwa Amaren kyautar sandunan da za su rika lakadawa mazan auren su duka a yayin da suka mare su ko suna cikin maye.

Rubuce a jikin sandunan, bayani ne mai taken “Maganin yan maye, kuma ba ruwan yansanda a ciki”

KU KARANTA:

A cewar ministan harkokin cikin gida, Gopal Bhargava ya shaidawa amaren su zage su suburbudawa mazan dukan tsiya a duk lokacin da suka gay a dace. “Idan mijinki ko wani dan uwansa ya dawo gida cikin maye, kiyi maganinsa da wannan sanda.”

An rabawa Amare 700 sandunan dukan mazajensu, idan sun bugu da giya
Sandunan dukan maza

A yanzu haka minista Bahgrava yayi odan sandunan dukan mazaje guda 10,000 dayake da niyyar raba ma sabbin amare.

Ministan yace manufar raba sandan shine don taimaka ma yan matan dake kauye wajen yaki da shan giya da maye.

“Matan kauye suna korafin a duka lokacin da mazajensu suka bugu sai su fara dukansu. ba wai mun raba wannan don tunzura mata bane, a’a don kare su ne.”

An rabawa Amare 700 sandunan dukan mazajensu, idan sun bugu da giya
A yayin bikn rabawa Amare 700 sandunan dukan mazajensu

Ko a yan kwanakin nan sai da gungun wasu mata suka kaddamar da aikin hana siyar da giya a garin Madhya Pradesh, sakamakon laifukan cin zarafin mata ya karu sosai a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2015.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani dan Najeriya ya kera abin mamaki

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: