Sule Lamido yana fuskanta shari’a a Dutse, babban birnin jihar Jigawa
- An tafi da tsararren tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido Dutse, wato babban birnin jihar domin fuskantar hukunci sakamakon furucin da yayi na rashin ladabi
- Yan sandar zone 1 ta tsare tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Lamido a Asabar din da ta wuce biyowa bayan korafi da gwamnatin jihar Jigawa tayi
Majiya daga jami’an tsaro a zone 1 sun fadawa Legit.ng cewa yansanda daukeda manya-manyan makamai ne suka raka dan gaban goshin PDP a tafiyar kimanin awa daya a motar Toyota Hilux zuwa makwantarsa a babban birnin jihar.
Wani daga jami’an tsaron a tafiyar tasu zuwa dutse ya sirrantawa Legit.ng akan yarjejeniyar kar a fadi sunansa cewa sun bar kano zuwa dutse a kimanin karfe 5.30 na safe.
KU KARANTA: 2019: Gwamnonin Jihohi 4 da sai sun yi da gaske
Ya kara da cewa a yanzu haka da nake maganar nan muna dutse domin tsaretsaren daya dace ta kara gano cewa an tsinkayar das u jami’an tsaron cewa magoya bayan shi tsohon gwamnan na iya tada zangazanga.
A tabbatar da hakan wakilin yansandan Zone 1, Sambo Dasuki yace, Lamido na Dutse ne domin fuskantar tuhuma.
Akwai rade-raden take cewa wanda wani tsohon gwamnan yana da aniyyar tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2019.
Ku biyo mu anan https://www.facebook.com/naijcomhausa/
Da anan https://twitter.com/naijcomhausa
Bidiyon shugaban kungiyar IPOB
Asali: Legit.ng