Wannan abu da me yayi kama: Gwamna ya tikawa wata ciki
– Akwai kishin-kishin din cewa wani Gwamna yayi wata mai hidimar kasa ciki
– Yanzu haka an yi kasar waje da wannan Budurwa
– Tana dauke da juna biyun wannan Gwamna
Ko ina Duniya za ta damu Jama’a?
Wani Gwamna ne dai ya jibgawa wata mai bautar kasa a Jihar sa ciki.
Yanzu an yi kasar waje da wannan baiwar Allah.
Legit.ng na samun labari daga wata mai suna Stella Dimokokorkus cewa wani Gwamnan Najeriya ya dirkawa wata Budurwa da ta ke aikin hidimar kasa a Jihar sa ciki. Stella dai tace ba za ta kama suna ba.
KU KARANTA: Ina nan zan tona asiri Inji Jonathan
Dimokokorkus ta bayyana cewa Budurwar tana yin aikin hidimar kasar ne a gidan Gwamnati wanda da aka je aka dawo Gwamnan yayi mata ciki. Kai karshen takaitawa dai wannan Budurwa ta haifi ‘yan biyu a kasar waje.
A can kasar wajen kuma Kungiyar wasan kwallon kafa ta Manchester United da ke Kasar Ingila tayi makokin ‘Yan Najeriya da su ka rasu wajen kallon wasan Kungiyar a Garin Kalaba.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng