Ana wahalar kudi: Dangote ya samu wata kazamar riba

Ana wahalar kudi: Dangote ya samu wata kazamar riba

– Dangote ya samu wata riba yayin da ake kuka a Najeriya

– Kamfanin sukarin Aliko Dangote ya ci riba matuka a bana

– Duk Nahiyar Afrika dai Alhaji Dangote bai da wari

Alhaji Aliko Dangote mai kudin Najeriya na cigaba da samun nasara a kasuwaci.

Kwanaki Dangote ya sauka daga jerin Attajirai 100 na Duniya.

Alhaji Dangote ne mutum na 105 a masu kudin Duniya.

Ana wahalar kudi: Dangote ya samu wata kazamar riba
Mai kudin Duniya Aliko Dangote

Legit.ng na samun labari cewa Alhaji Aliko Dangote ya samu wata riba a wajen harkar sukari a shekarar bara na sama da Naira Biliyan 14. A halin yanzu dai Najeriya na cikin matsi na tattali wanda har shi Dangote bai tsira ba.

KU KARANTA: Gumi ya sabawa Sarkin Kano

Ana wahalar kudi: Dangote ya samu wata kazamar riba
Kamfanin Dangote ya samu riba bara

A lissafin da aka buga a karshen bara kurum Kamfanin sukarin Dangote ya samu riba kurum ta Naira Biliyan 14.4 wanda wannan idan ma an cire haraji da sauran hakkoki kenan. Wannan dai ba karamar nasara ba ce a kasuwa.

Shi dai Alhaji Aliko Dangote ne ya bayyana wannan da kan sa a wani taro da aka yi a Legas. Ribar na da alaka da tashin farashin kaya a kasuwa. Yanzu dai Dangote na ta shirin kammala katafaren aikin matatar mai a Legas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda ya kamata ayi da Barayin Gwamnati

Asali: Legit.ng

Online view pixel