Wani shehin malami ya rasu yana cikin karatun Al-Qur’ani
- Wani shehin malami ya rasu yana cikin karatun Al-Qur’ani a kasar Indonesia
- Rahotanni sun kawo cewa Abdulrahman ya samu bugun zuciya a lokacin da yake karatun
Sheikh Ja’far Abdulrahman, wani makarancin Al-Qur’ani na kasar Indonesia ya rasu a yayinda yake karatun Al-Qur’ani a gurin wani taro.
An bayyana cewa Abdulrahman ya samu bugun zuciya a lokacin da yake karatun.
Masu sauraro sukayi gaggawan kai masa taimako sannan kuma aka dauke shi cikin gaggawa.
KU KARANTA KUMA: Obasanjo ya bayyana dalilinsa na zaɓan Jonathan don zama mataimakin Yar’adua
Ya fadi ne a lokacin da yake karanta suratul Al-Mulk.
Abun tausayi ya rasu ne a gurin wani taro, wanda ministan kula da al’amuran Indonisia ya shirya.
Rasuwar Abdulrahman ya bazu a kafofin watsa labarai, kamar yadda masu sharhi ke fadin cewa ya dace sosai domin ya rasu a kan tafarki madaidaciya a halin yana cikin karatun littafi mai girma.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wanene ba barawo ba a yan siyasan Najeriya?
Asali: Legit.ng