EFCC ta gabatar da shaidu 18 a shari’ar Sule Lamido da yayansa
- Sule Lamido ya bukaci a sauya Alkalin dake sauraron karar da EFCC ta shigar da shi
- Lauyan EFCC Abubakar M.S ya nuna rashin gamsuwa da hakan
Hukumar yaki da almundahana da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido gaban babban kotu dake birnin tarayya Abuja dake karkashin alkali mai shari’a Babatunde O. Quadri a ranar Laraba 26 ga watan Afrilu.
Sai dai lauyan Sule Lamido Joe Agi ya bukaci kotun data mayar da sauraron karar zuwa ga tsohon alkalin daya fara sauraron karar mai shari’a Ademola Adeniyi. Dama dai Ademola ne ya fara sauraron karar, amma daga bisani sai hukumar alkalai ta kasa ta dakatar da shi kan zargin wwasu badakala dake kansa.
KU KARANTA: Shugaban jam’iyyar APC ya gana da gwamnoninsa
Yayin sauraron karar tuhume tuhume da suka danganci almundahana akan Lamido da yayansa Aminu Sule Lamido; Mustapha Sule Lamido; Aminu Wada Abubakar da kuma kamfanunuwansu, Bamaina Holdings Limited and Speeds International Limited , lauyan EFCC ya gabatar da shaidu 18.
Sai dai sakamakon bukatar da lauyan Lamido ya mika ma kotun, kotu ta bukaci da’a saurara har sai sun ji daga bakin alkalin alkalai na kasa kan batun wanene zai cigaba da sauraron karar, tunda dai a yanzu haka wata kotun ta wanke Alkali Ademola Adeniyi daga zargin cin hanci da rashawa.

Amma lauyan EFCC M.S Abubakar ya nuna damuwarsa, kuma ya nuna rashin amincewarsa da bukatar lauyan Sule Lamido, don haka ya bukaci kotu data cigaba da sauraron karar har sai lokacin da alkalin alkalai ya yanke hukunci.

Legit.ng ta ruwaito bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai alkali Babatunde ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar Laraba 3 ga watan Mayu na 2017.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
EFCC ta tasa keyar Andrew Yakubu zuwa kotu
Asali: Legit.ng