Tsohon Gwamna Jihar Neja ya kare a kurkuku
– Kotu ta bada umarni a jefa Muazu Babangida Aliyu cikin gidan yari
– Babangida Aliyu yayi Gwamna na shekaru 8 a Jihar Neja
– Haka-za-lika Kotu ta sa a garkame Umar Nasko
Legit.ng ta samu labarin yadda aka yi kotu ta bada umarni a damke tsohon Gwamnan Jihar Neja Muazu Babangida Aliyu.
Kotu ta tsare Dan takarar Gwamnan Jihar a zaben da ya wuce watau Umar Nasko.
Za su sha zaman kaso na kwanaki 10 a gidan maza.
Ana zargin Talban Minna Dr. Muazu Babangida Aliyu da karkatar da wasu kudi sama da Naira Biliyan 4.5 na Jihar zuwa aljihun sa. Hukumar EFCC mai yaki da zamba ce dai ta maka Gwamnan da wasu dabam a Kotu.
KU KARANTA: An wulakanta wani Sarki a taro
Ana zargin tsohon Gwamnan da laifuffuka har 6 na satar kudi, cin amana da sauran su. Alkalin y adage karar zuwa watan gobe inda yace za a cigaba da shari’ar a kowace rana ta Allah. Yanzu dai ko tsohon Gwamnan zai sha?
Kuna da masaniya cewa an yi kira ga Gwamnonin Jihohin Najeriya su yi koyi da Gwamnatin Tarayya wajen dabagga tsarin nan na asusun bai daya watau TSA.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kotu ta saki Nnamdi Kanu na Biyafara
Asali: Legit.ng