Hukumar INEC ta tsai da ranar sake zabe a jihar Katsina
- Hukumar zabe ta shiyar Katsina ta ce ta tsai da ranar 20 ga watan Mayu a matsayin ranar sake zaben mazabar Mashi / Dutsi ta tarayya
- Kura ya ce jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaben fitar da dan takara tsakanin watan Mayu 1 zuwa 4, 2017
- Kura ya tabbatar da cewa za a fara gangamin kamfen daga watan Mayu 5 da kuma kawo karshe a ranar 19 na watan
Hukumar zabe mai zaman kansa (INEC) ta tsai da ranar 20 ga watan Mayu a matsayin ranar sake zaben mazabar Mashi / Dutsi ta tarayya a Jihar Katsina.
Legit.ng ta ruwaito cewa za a yi wannan zaben cika gurubin mazabar ne sanadiyar rasuwar dan majalisar mai wakiltar mazabar, Alhaji Sani Bello a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2017.
Jami’in hukumar, Mista Yunusa Kura ya bayyana haka a ranar Laraba, 26 ga watan Afrilu a Katsina a lokacin wata taron ruwa da tsaki a jihar.
KU KARANTA KUMA: Har yanzu babu kasafin kudin wannan shekarar a Najeriya
Kura ya ce a na sa ran jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaben fitar da dan takara tsakanin watan Mayu 1 zuwa 4, 2017.
Ya ce jam'iyyun siyasa za su fara gangamin kamfen daga watan Mayu 5 da kuma kawo karshe a ranar 19 na watan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yadda hukumar EFCC ta gurfanar da wasu jami'in hukumar zaben na INEC a kotu a cikin wannan bidiyo
Asali: Legit.ng