“Fasahar zamani zata samar da ayyukan yi sama da miliyan 3” – inji Sheikh Fantami
- Shugaban hukumar kimiyya ta kasa, NITDA yace gwamnati zata maye gurbin man fetur da ilimin kimiyya
- Dakta Fantami ya bayyana cewa za'a iya samun ayyuka miliyan 3 daga kimiyya da fasaha
Hukumomin Najeriya sun ce fasahar zamani zata samar da ayyukan yi sama da miliyan 3 da kuma kudaden shiga ga kasar da yawansu ya kai Dala biliyan 88 nan da shekaru 10 masu zuwa.
Gidan Rediyon Faransa ta ruwaito ministan kasuwancin Najeriya Dr Okechukwu Enelamah, yana bayyana hakan a wajen wani taron ministocin kasashe masu tasowa da ake gudanarwa a birnin Geneva karkashin majalisar dinkin duniya.
KU KARANTA: “Buhari ba shi da isashshen lafiya, ya koma gefe ya huta” – Inji Makarfi
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Enelamah yana cewa “Najeriya na da dimbin matasan da suka yi fice a fannin kere kere da sadarwa wanda zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.”
Yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI, Dr Isa Ali fantami, shugaban hukumar NITDA dake kula da fasahar zamani a Najeriya ya ce lokaci yayi da Najeriya zata kauracewa dogaro da man fetur domin karfafa tattalin arzikinta, idan aka yi la’akari da halin da kasar ta fada na matsin tattalin arziki sakamakon dogaro kan abu daya.
Dr Fantami yace: “Fasahar na’ura mai kwakwalwa na kan gaba wajen hanyoyin da zasu taimakawa Najeriya wajen samar da ayyukan yi.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wani dan Najeriya yace yayi nadamar zaban APC, ba shi da aiki
Asali: Legit.ng