Da shugabannin yanzu za su yi koyi da halayyar Sardauna, babu shakka da Najeriya ta zauna lafiya - Inji Maitama Sule

Da shugabannin yanzu za su yi koyi da halayyar Sardauna, babu shakka da Najeriya ta zauna lafiya - Inji Maitama Sule

- Alhaji Yusuf Maitama Sule dan masanin Kano ya shawarci shugabannin yanzu da zu yi koyi da halayen kwarai na Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello

- Maitama Sule ya ce a zamanin mulkin marigayi Sardauna kasar arewa tana matsayin yanki guda ne

- Gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim Shetima ya yi fatan su a matsayinsu na shugabanni a yanzu, za suyi koyi da wasu halayya irin na marigayi Sardauna

An tabbatar da cewar da shugabannin Nijeriya na yanzu za su yi koyi da halayen kishin kasa irin na marigayi Gamji dan kwarai Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, to ko shakka babu da kasa Najeriya da jama'arta sun zauna lafiya da samun ci gaba.

Sanannen dattijon nan mai kishin yankin arewa Alhaji Yusuf Maitama Sule dan masanin Kano ya bayyana hakan lokacin dayake jawabi a yayin wani gagarumin taro na tunawa da marigayi Firimiyan jihar arewa Sir Ahmadu Bello Sardauna, wanda gidauniyar tunawa da Sardauna dake kaduna ta shirya, kuma ya gudana a babban dakin taro na cibiyar dake kaduna.

Maitama Sule ya cigaba da cewar, a zamanin mulkin marigayi Sardauna kasar arewa tana matsayin yanki guda ne, kuma dukkanin jama'ar yankin babban burinsu shine a kira da sunan 'yan arewa, a wancan lokacin babu bambanci a tsakanin dan kabilar Igala ko Tibi ko Gwari da Idoma da al'ummar Hausa/Fulani, kuma a haka Sardauna yayi rayuwarshi ta gina arewa har takai ga matsayin tserewa takwarorinta, kuma bai gushe akan wannan matsayi ba har ta Allah ta kasance a kanshi.

Da shugabannin yanzu za su yi koyi da halayyar Sardauna, babu shakka da Najeriya ta zauna lafiya - Inji Maitama Sule
Marigayi Gamji dan kwarai Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto

Legit.ng ta ruwaito cewa dan masanin na Kano ya kuma bukaci shugabanni da ake dasu yanzu a nan arewa kamar gwamnoni 'yan majalisu da sauransu dacewar suyi koyi da halayen kwarai na Sardauna, dominsu kasance abin koyi da kwatance anan gaba.

KU KARANTA KUMA: Kamannin shugaba Buhari ya yi bikin murnar ranar haihuwarsa a Abuja

Lokacin da yake jawabi shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim Shetima, ya bayyana salon shugabanci irin na Sardauna, a matsayin ruhi wanda ke raya jama'a, inda yayi fatan su a matsayinsu na shugabanni a yanzu, za suyi koyi da wasu halayya irin na marigayi Sardauna, musamman na rashin nuna kabilanci ko bambancin addini ga jama'ar da suke shugabanta domin samun nagartattun jama'a.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali yadda sariki Sanusi ya caccaki shugabanin Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng