Darajar Naira ta karu a kasuwa

Darajar Naira ta karu a kasuwa

– Farashin Naira ya karu a kasuwar canji

– Ma’ana Dalar Amurka ta yi kasa

– CBN ya saki sama da Dala miliyan 200

Legit.ng na samun labari cewa darajar Naira ya dan daga sama a jiya bayan da Nairar ta sha kasa a farkon wannan makon. Babban bankin kasar CBN ya saki sama da Dala miliyan 200 domin tsagaita tashin dalar.

Darajar Naira ta karu a kasuwa
Naira ta kara daraja a kasuwa

CBN Babban bankin kasar na cigaba da kokarin ganin maganin tashin dalar inda aka kawo sababbin tsare-tsare na sakin dalar ga ‘yan canji da sauran masu bukata kai-tsaye ba tare da bi ta hannun ‘yan kasuwa ba.

KU KARANTA: Naira tayi raga-raga a kasuwa

Darajar Naira ta karu a kasuwa
Dala ta sha kasa a hannun yan kasuwa

Yanzu haka CBN ta saki Dala Miliyan 246.2 a Ranar Litinin. A karshen makon jiya dai an saida Dala kan N385 wanda ya daga a farkon makon nan zuwa N390 a hannun ‘yan kasuwa. Yanzu haka dai Dalar ta koma N382 inda aka samu ragi.

Mista Isaac Okoroafor ya bayyana cewa sabon tsarin da aka kawo zai taimaka wajen samar da Daloli ga masu bukata cikin sauki. A wancan makon farashin EURO yana kan N410 yayin da Pound Sterling na kasar Ingila yake N495. Yanzu dai suna kara sauka kasa ba laifi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yanayin farashin kaya a Jihar Ogun

Asali: Legit.ng

Online view pixel