Ruwan sama mai iska ya tafi da gidaje a jihar Nasarawa
-Anyi wata ruwan sama mai ban mamaki a garin Keffin jihar Nasarawa
-Ba’a samu rahoton rashin rai ba har yanzu
Wata ruwa mai karfi da iska da akayi a garin Keffi jihar Nasarawa ya lalata gidaje da kuma tuge bishiyoyi.
Wani manemi labarai da ya zagaya garin bayan ruwan saman mai karfin , ya lura ruwa ya tai da rufin gidan mutane kuma ya tuge bishiyoyi ta jefa su kan titi.
Jaridar Legit.ng ta bada rahoton cewa wannan abu ya kawo cikas ga wucewan motoci akan titi kana kuma ya tuge falwayan wuta inda ya iska ya jefasu gidajen mutane.
Inda abin yafi shafa shine babban asibitin gwamnati da kuma kasuwa inda aka ga mutane suna karye reshinan bishiyoyin da suka fado.
KU KARANTA: Sarki Sanusi ya mayar da martani akan zargin da ake masa
Wata mazauniyar garin, Mrs. Fausat Jamaa, tace wannan ruwa ya sababba batada inda zata kwana da iyalinta.
“Raina na bace yau. Rufin gidana ya fita. Yanzu ban san abinda zanyi ba,” Tace.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng