Messi ya kafa tarihi a kan Real Madrid, ya zura kwallon sa ta 500

Messi ya kafa tarihi a kan Real Madrid, ya zura kwallon sa ta 500

- Lionel Messi ya samu nasarar ci wa kungiyarsa ta FC Barcelona kwallo ta 500, a tsawon lokacin da ya shafe yana fafatawa kungiyar tasa wasanni

- Kwallon ta 500 din da Messi ya ci ta bai wa Barcelona damar samun nasarar kan Real Madrid da kwallye 3-2 a karawar da suka yi a jiya Lahadi

Kwallaye biyun da Messi ya zura a ragar Madrid ya kawo karshen shekaru uku da dan wasan ya shafe ba tare da ya samu nasarar jefa kwallo a ragar Madrid ba, a duk lokacin da kungiyoyin biyu zasu kara.

Legit.ng ta samu labarin cewa a sauran wasannin da aka kara a gasar Laliga ta Spain kuwa, Real Sociedad ta samu nasara kan Deportivo La Cruna da 1-0, sai Celta Vigo da tayi rashin nasara a hannun Real Betis da 1-0 yayinda Las Palmas da Alaves suka tashi 1-1 a wasan da suka fafata.

A tsayuwar Teburin gasar Laligar kuwa, Barcelona ke kan gaba da maki 75, Real Madrid na biye mata itama da maki biyar wadda kuma take da kwantan wasa sai kuma kungiyar Atletico Madrid a matsayi na da maki 68.

Messi ya kafa tarihi a kan Real Madrid, ya zura kwallon sa ta 500
Messi ya kafa tarihi a kan Real Madrid, ya zura kwallon sa ta 500

KU KARANTA: Bangarorin Boko Haram na yakar juna

Kungiyoyi uku na karshe kuwa sun hada da Sporting Gijion ta 18 da maki 23, Granada ta 19 da maki 20 sai kuma Osasuna da ta dauki teburin a ka a matsayi an 20 da maki 18.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: