Bill Gates ya hana yaran sa su rike wayar salula

Bill Gates ya hana yaran sa su rike wayar salula

– Attajirin Duniya Bill Gates yace bai barin kananan ‘ya ‘yan sa su mallaki waya

– Bill Gates yace sai sun girma yake ba su damar samun tarho

– Mr. Gates dai yace agogon hannun sa bai wuce Dala 10 ba

Bill Gates ya hana yaran sa su rike wayar salula
Kwanaki da Bill Gates ya zo Najeriya

Tun shekaru 23 da suka wuce Bill Gates yake cikin Attajiran Duniya to sai dai duk da haka agogon da yake daurawa bai wuce Dala 10 rak ba kamar yadda Legit.ng ta samu labari daga wata Jaridar Amurka.

Bill Gates da matar sa Melinda suna da ‘ya ‘ya 3 ne rak a Duniya inda babban ke da shekaru 20. Mr. Gates yace bai bari yaran su taba rike waya sai sun kara girma sun kai shekara 14. Bill Gates ne dai wanda ya kirkiro manhajar Microsoft a Duniya.

KU KARANTA: Wani Sanatan Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Bill Gates ya hana yaran sa su rike wayar salula
Bill Gates tare da iyalin sa

Mai kudin Duniyan yake cewa kuma ba kasafai yake bari yaran su rike waya ba a ko da yaushe musamman cikin dare lokacin barci. Bill Gates yace hakan zai taimaka masu kwarai da gaske a rayuwar su.

Duk Duniya a wannan shekarar ma dai kasurgumin Attajirin ne ya fi kowa kudi a Duniya. Arzikin Bill Gates ma dai karuwa yayi daga Dala Biliyan 75 zuwa Dala Biliyan 86 a bana. Duk da haka Bill Gates bai wasa da tarbiyyar iyalin sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda wata mata ta ke facin mota a Kwara

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng