Hukumar sojin sama ta gwada rokan da ta kera da kanta a Najeriya

Hukumar sojin sama ta gwada rokan da ta kera da kanta a Najeriya

- Hukumar sojin sama tayi gwajin rokan da aka kera a gida

- Hukumar sojin Najeriya NAF ta samu nasaran harba roka mita 30.1mm daga kasa zuwa sama wanda jami’ an bincikenta suka kera

An gwada rokan ne inda aka harba ne inda suka hadu a Kwenev, Makurdi domin murnan zagayowar hukumar na 53.

Kana kuma ta kera maharban jirgin kasa na roka. Rokan tana iya harba kanta ta wata manhaja da tayi. Banda baja kolin wasan wuta a sama, an nuna wata gagarumin yadda ake kai makaman hukumar.

Jiragen da akayi amfani da su ya kunshi Augusta 109 LUH, L-39ZA, Alpha Jet da F-7Ni.

Hukumar sojin sama ta gwada rokan da ta kera da kanta a Najeriya
Hukumar sojin sama ta gwada rokan da ta kera da kanta a Najeriya

A jawabinsa, shugaban hukumar tsaron Najeriya, Janar Gabriel Olonisakin ya taya hukumar sojin saman murna akan bikin ta na 53 kuma yabawa shugabancin NAF da bunkasa ilimin hafsosinta.

“A yau, ina alfaharin cewa NAF ta burgeni. Wannan shirye-shiryen da kai kawon makamai daga wurare daban-daban ya cancanci yabo.”

KU KARANTA: Hukumar DSS ta kai simame odinshin PenCom

Janar Olonishakin ya bayyana cewa Najeriya zata iya alfahari da hukumar sojin saman ta wajen nuna karfin sojan sama kamar yadda aka gani a yankin arewa maso gabas inda ta taimakawa jami’an sojin kasa.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel