Ban da ni cikin wadanda aka jefa a Katsina - inji Honarable Aminu Tukur
- Dan majalisa mai wakiltan Bakori da Danja jihar Katsina, Amiru Tukur yace bashi acikin wadanda suka sha ruwan duwatsu a taron jam’iyyar da akayi a garin Funtua.
- Amiru ya sanar mana da haka ne da yake zantawa da wakili majiyar mu na majalisar Wakilai Nasiru Ayitoro.
“Babu wanda ya kai mini hari a wannan taro, duk da cewa naji wai an kai ma wasu manyan baki hari a taron.
“Ni ma ji nayi cewa wai an kai wannan hare-hare a lokacin da abokanai na da ‘Yan’uwa suke ta kira na domin yi mini jaje cewa wai sunji an har-harbe ni. Na gaya musu ba haka bane domin ni bana wajen taron a lokacin da hakan ya faru. Kamar yadda ka ganni yanzu haka lafiya na lau. Kuma ka sani cewa wannan tashin hakali ya faru ne a Funtua kuma ni ina wakiltan Bakori ne da Danja."
Legit.ng ta samu labarin cewa Sanata mai wakiltan Katsina ta Kudu da dan majalisan da ke wakiltan Kananan hukumomin Bakori da Danja a majalisar wakilai sun sha da kyar a taron jam’iyyar APC da akayi a garin Funtua.
Kamfanin dillancin labarai ta rahoto cewa jami’an ‘yan sanda ne suka kawo musu dauki da ya hada da tawagar gwamnan jihar Aminu Bello Masari.
Sun sha ruwan duwatsu da takalma a harin inda sai da akayi amfani da barkonun tsohuwa kafin aka samu shawo kan matasan.
KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kai wa sojojin Najeriya harin ba zata
Gwamna Masari da sanata Abu Ibrahim suna halartar taron karban wasu ‘Ya’yan jam’iyyun PDP, APGA da PDM ne da suke canza sheka zuwa jam’iyyar APC.
Ba’a dade da fara taron ba kwatsam sai matasa suka fara ihun “Ba ma son Abu Ibrahim ba ma so” sai suka fara jefar bakin da duwatsu da takalma.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Ga wani matashi nan na bada ra'ayn sa game da yan siyasar mu
Asali: Legit.ng