Ka ji irin amfanin dabino a jikin mutum
– Kayan marmari su na da amfani kamar yadda mu ka fara fada maku
– Dabino na da amfani a jikin Adam kwarai da gaske
– Kadan daga ciki akwai maganin cutar sikila, kansa da sauran su
A jiya muka kawo maku irin amfanin kayen marmari kamar su abarba da sauran su. Ita Abarba na maganin cutar nan ta atiraitis mai damun gabbai da cancer da sanyi sannan kuma tana kara kaifin gani da kuma hakora.
Haka kuma dabino na da amfani matuka daga ciki:
1. Maganin gudawa
Dabino na maganin cutar gudawa da duk wani ciwo ko lalacewar ciki da ake fama da shi.
2. Cancer
Haka kuma dabino na maganin cutar nan ta ’Cancer’ mai kashe kwayoyin garkuwa.
KU KARANTA: Ashe mangwaro na da amfani haka?
3. Dabino na kara lafiya
Dabino na kara lafiya inda yake karawa mutum kiba saboda wasu sinadarai da yake kunshe da su.
4. Dabino na kara karfi
A dalilin irin sindaran da ke ciki na Calcium, Sulphur, Iron da sauran su, Dabino na kara karfi har kwanjin mutum ya karu.
Shi ya sa ma dai ake son cin dabino da zaran masu abinci sun sha ruwa domin kuwa yana kara karfi. Haka kuma ake ba yaro da zarar an haife sa.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Farashin kayan abinci a Najeriya
Asali: Legit.ng