Shugaban NIA, Oke baiyi kuka ba bayan an dakatar da shi – Fadar shugaban kasa

Shugaban NIA, Oke baiyi kuka ba bayan an dakatar da shi – Fadar shugaban kasa

- Mataimakin shugaban kasa a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyana rahotannin kafofin watsa labarai na cewa shugaban hukumar NIA, Ayo Oke yayi kuka bayan ya samu labarin dakatar da shi a matsayin rashin adalci.

- Garba Shehu ya ce shugaban baiyo kuka ba kamar yadda ake yayatawa a kafofin watsa labarai

- Kakakin ya bayyana cewa babu wanda zai niya ganin Ayo Oke yana kuka kamar yadda ya kasance a cikin motar SUV mai bakin gilashi a tagogin

Fadar shugaban kasa ta karyata rahotannin kafofin watsa labarai dake cewa darakta janar na kungiyar leken asiri na kasa da aka dakatar, Ayo Oke, yayi kuka bayan ya samu labarin dakatar da shi.

Legit.ng ta tuno cewa an rahoto cewa darakta janar na hukumar NIA ya yi kuka a yayinda yayi kokarin shiga fadar shugaban kasa, bayan an dakatar da shi a ranar Laraba, 19 ga watan Afrilu.

Amma babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu wadda yayi magana kan al’amarin a Abuja a ranar Alhamis, 20 ga watan Afrilu, ya bayyana rahotannin a matsayin rashin adalci.

Shugaban NIA, Oke baiyi kuka ba bayan an dakatar da shi – Fadar shugaban kasa
Fadar shugaban kasa ta ce Shugaban NIA, Oke baiyi kuka ba bayan an dakatar da shi ba

Ya bayyana cewa idon shaida na ziyarar da Oke ya kai ga mataimakin shugaban kasa a wannan rana da kuma asusun say a nuna karara cewa shugaban baiyi kuka ba kamar yadda ake ta yayata wa a kafofin watsa labarai, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Ba mu halarci bikin auren 'yan luwadi a Zaria ba

Legit.ng ta tuno cewa a ranar Laraba mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya gana da babban sakataren gwamnatin tarayya, Mista Babachir Lawal da shugaban hukumar leken asiri, Ayo Oke daban-daban sa’a daya kafin a sanar da dakatar da Lawal da Oke daga aiki.

Babban sakataren gwamnatin tarayya ya ki yin sharhi a kan ganawar sa da mataimakin shugaban kasa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Shin shugaban kasa Buhari ya fitar da Najeriya daga koma bayan tattalin arziki?

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng