Guguwa mai Ƙarfi ta lalata gidaje fiye da 150 a garin Ɗadin Kowa na Arewa

Guguwa mai Ƙarfi ta lalata gidaje fiye da 150 a garin Ɗadin Kowa na Arewa

- Sama da Gidaje 150 wata iska mai ƙarfin gaske ta lalata a garin Dadin Kowa dake ƙaramar hukumar Yamaltu Deba ta jihar Gombe

- Jami’in yaɗa labarai na masauratar yankin ya faɗawa manema labarai a Dadin Kowa yau Laraba yace guguwar ta fara ne a ranar litinin da daddare da misalin ƙarfe 10 na dare ta kuma shafe kimanin sa’a guda

Yace babu waɗanda suka rasa rayukansu,amma wasu daga cikin mutanen sun samu raunuka kamar yadda wasu da yawa suka rasa matsugunansu.

Legit.ng ta ruwaito cewa yace tunda iftila’in ya faru babu wani jami’in gwamnati da ya ziyarci yankin domin bada tallafi ko kuma jajantawa al’ummar yankin.

Mijinyawa yace sakataren masarautar yana tattara bayanai domin ya miƙawa hukumar bada a gajin gaggawa ta jihar.

Guguwa mai Ƙarfi ta lalata gidaje fiye da 150 a garin Ɗadin Kowa na Arewa
Guguwa mai Ƙarfi ta lalata gidaje fiye da 150 a garin Ɗadin Kowa na Arewa

Waɗansu da iftila’in yafaru akansu sun faɗawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa cewa yanzu basu da muhalli,kana sunyi kira ga hukumomin da abun ya shafa dasu kawo musu agaji.

Ɗaya daga cikinsu Malam Tanimu Adamu yace gidansa ga baki ɗaya ya rushe sannan matansa da yaransa sun samu raunuka.

KU KARANTA: Yan fashin teku sun kashe sojojin Najeriya 2

Da yake magana kan lamarin Mal Ibrahim Nalado jami’i a hukumar bada agajin gaggawa ta jihar yace hukumar bata da labarin abinda yafaru.

Yace zasuje Ɗadin Kowa domin duba irin ɓarnar da guguwar tayi kafin su san irin tallafin daza su bayar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma ku kalli tattaunawa da wasu yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: