Dubi sana’ar da wani matashi ya koma bayan ya kammala Digiri

Dubi sana’ar da wani matashi ya koma bayan ya kammala Digiri

– Wani Saurayi ya koma makanikin karfi da yaji bayan yayi Digiri

– Wannan bawan Allah yayi karatun Digiri a Jami’a

– Sai dai yanzu hanyar abincin sa tana wurin gyaran motoci

Dubi sana’ar da wani matashi ya koma bayan ya kammala Digiri
Kowa da sana’ar da ta karbe sa Inji Hausawa

Legit.ng na samun labarin wani bawan Allah da ya koma gyaran motoci bayan ya kammala karatun Digiri a Jami’ar Obafemi Awolowo. Abin mamaki wannan ta’aliki dai ya karanci ilmin sha’anin tattalin arziki ne.

Taiwo Abiri mutumin Garin Ibadan ne wanda yayi wa kanikanci haye bayan yayi karatun Digiri. Yanzu haka wannan matashi ya hada sama da Naira miliyan 25 wajen gyaran motoci. Da Taiwo na da niyyar komawa karatu amma yanzu ya fasa.

KU KARANTA: Tofa: Wani Gwamna ya sha ruwan duwatsu

Dubi sana’ar da wani matashi ya koma bayan ya kammala Digiri
Wani makaniki a bakin aiki

Abiri dai bai taba koyon harkar gyaran mota ba sai daga bayan ya bar aikin sa a wani kamfani ya koma koyon sana’ar kanikanci. Abiri ya kan kuma nemi bidiyo ya a yanar gizo ya kalla ta haka har ya kware yanzu yayi kudi.

Babban dan wasan Juventus G. Chiellini ya kammala karatun Digirin sa na biyu a fannin harkar kasuwanci watau M. BA. Dan kwallon yayi karatun ne a Jami’ar Turin ta kasar da ke cikin Birnin da Kungiyar Juventus ta ke.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko ka taba ganin mace da aikin kanikanci?

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng