Madalla! Sojoji a Nijer sun samu nasarar kashe yan Boko Haram 57
- Wata majiyar tsaro a Nijar ta ce sojojin kasar sun kashe mayakan Boko Haram akalla 57 a wata musayar wuta da suka yi a kusa da garin Gueskerou
- Garin yana cikin Jihar Diffa yankin kudu masu gabashi da ke kan iyaka da Najeriya.
Legit.ng ta samu labarin cewa akwai babban kwamandan Boko Haram daga cikin mayakan da aka kashe, kamar yadda majiyar sojin ta tabbatarwa kamfanin dillacin labaran Faransa.
Sojojin Nijar sun yi nasarar fatattakar yan Boko Haram ne bayan sun shigo garin cikin mota da Babura a ranar Lahadi.
Majiyar da ta tabbatar da labarin ta ce akwai sojoji da dama da suka samu rauni a musayar wutar.
Sannan Sojojin sun yi nasarar kwato tarin makamai daga hannun mayakan na Boko Haram.
KU KARANTA: Anyi mummunan artabu tsakanin yan sanda da yan shi'a
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Nan ma dai wasu mutane ne da suka tsere wa rikicin Boko haram
Asali: Legit.ng