Kalli ɓula-ɓulan kayan marmari da aka samu a gonar Buhari a Daura

Kalli ɓula-ɓulan kayan marmari da aka samu a gonar Buhari a Daura

- Manufar gwamnatin Buhari na habbaka noma a Najeriya ba a baki bane kadai

- An noma wasu ɓula-ɓulan kayan marmari a gonar Buhari dake garin Daura

Aniyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yin noma haikan a Najeriya tare da karkatar da akalar tattalin arzikin kasar nan zuwa ga noma ba a baki bane kadai, har a aikace shugaban yana gudanar da aniyar, kamar yadda aka gani a gonarsa dake Daura.

Diyar shugaba Buhari, Zahra Buhari ta daura hotunan wasu maaka-maakan kayan marmari da aka noma su kuma aka girbo su daga gonar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake garin Daura na jihar Katsina.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta alanta sabon tsarin habaka noman da Timatur a Najeriya

Zahra Buhari tayi ma hotunan taken kai tsaye daga gonar baba, #Gonar Daura #Manyan Kankana: kamar yadda Lindaikejisblog ta ruwaito.

Kalli ɓula-ɓulan kayan marmari da aka samu a gonar Buhari a Daura
Zahra Buhari dauke da kankanan

Kayayyakin marmarin sun hada da Kankana, da sauransu.

Sai dai abinka da yan Najeriya da basa ganin zare basu tsinka ba, Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin tsokacin da wasu yan Najeriya sukayi dangane da hotunan;

Kalli ɓula-ɓulan kayan marmari da aka samu a gonar Buhari a Daura
bula-ɓulan kayan marmari da aka samu a gonar Buhari a Daura

Wani cewa yayi: “Da ace inda da kudi, da sai nawa noman yafi wannan kyau!

Wani kuma yace:“Wannan yayi kyau, Allah yasa albarka cikin abin da aka girba.”

Daga baya wani sai yace: “Kawai yaci abinsa ba sai ya ishe mu da surutu ba.” Inda aka samu shi kuma tambaya yake yi, “shin Zahra Buhari, me yasa ba kya zaman a gidan mijinki?”

Kalli ɓula-ɓulan kayan marmari da aka samu a gonar Buhari a Daura
Kankana daga gonar Buhari

Daga karshe wani mai suna Fresh cewa yayi: “Yayin da mutumin arzikin nan ke kokarin girbe abinda ya shuka a gonarsa, Patience Jonathan zuwa banki tayi don ta cire kudin sata. Wai shin littafin Bible din da masu da’awar addinin kirista suka raba a jihatr Bayelsa bai cika bane?”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon nan don sanin farashin kayayyakin marmari a kasuwa;

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng