Sarkin Kano ya yi barazanar rusa gidan Kadiriyya
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi barazanar rushe shalkwatar Darikar Kadriyya
- Ya kalubalanci 'ya'yan tsohon shugaban Darikar da su hada kawunansu
- Sarki Sanusi ya jinjina wa Malam Nasiru Kabara kan yadda ya ke jagorantar mutane a lokacin da yake raye
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya yi barazanar rusa shalkwatar Darikar Kadriyya ta Afrika ta Yamma da ke birnin, muddin ‘ya'yan tsohon shugaban Darikar marigayi Sheikh Nasiru Kabara suka gaza wajen hada kawunansu.
Muhammadu Sanusi II ya yi wannan barazana ce lokacin da daya daga cikin 'ya'yan marigayin Nasiru Kabara, Sheikh Askiya Nasiru Kabara ya ziyarce shi a fadarsa.
KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya bayyana kudin albashinsa, ya kalubalanci majalisan dokokin tarayya ta bayyana na ta
Tun bayan nada sabon shugaban Darikar Kariballa Nasiru Kabara ake ci gaba da samun sa-in-sa tsakaninsa da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Legit.ng ta samu labarin cewea Sarkin na Kano ya bayyana takaicinsa ganin yadda ‘yayan na Nasiru Kabara suke rikici da juna, in da ya bayyana cewa kowanne daga cikinsu na iya wakiltar mahaifin nasu a maimakon takun saka da juna.
Sarki Sanusi ya kuma jinjina wa Malam Nasiru Kabara kan yadda ya ke jagorantar mutane kimanin miliyan 1 a bikin hawan maukibi a lokacin rayuwarsa ba tare da samun tashin hankali ba.
Sannan ya kara da cewa daukan matakin rusa gidan marigayin don gina masallaci ya fi alheri fiye da yadda 'ya'yansa ke kokarin wargaza abin da ya bari.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Legit.ng ta kawo maku bidiyon Sarki Sanusi da ya soki shugabannin Najeriya.
Asali: Legit.ng