Farashin shinkafa zai fadi zuwa N6000
- Manoman shinkafar gida sun sanar da cewa farashin shinkafa zai sauka zuwa N6000
- Manoma na cikin shirin masu karban bashi daba CBN don kara samar da wadataccen abinci
- Bukatar shinkafar gida ya karu
Ana saka ran cewa farashin shinkafa zai fadi zuwa N6000 a cikin watanni shidda masu zuwa a cewar Alhaji Aminu Goronyo wanda ya kasance shugaban kungiyar manoman shinkafa na Najeriya (RIFAN).
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa yaki da cin hancin Gwamnatin Buhari ke samun cikas-Obasanjo
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Goronye yayi magana a karshen mako inda yace manoma sun tsananta samar da shinkafa da wannan ne farashin shinkafa zai sauka.
Yace ayanzu aka siyar da shinkafa kasa da farashi N10000 a wasu jihohin arewa sannan kuma cewa yawan bukatar shinkafar ta shafi manoma ta hanya mai kyau.
Legit.ng ta tattaro inda Shugaban kungiyar na RIFAN ya bayyana cewa manoma da daman a amfani da damar shirin bayar da bashi da babban bankin Najeriya (CBN) keyi sannan kuma cewa kungiyar san a daukar manoma da dama don su shiga shirin.
Ya ce yana sa ran farashin shinkafa zai ci gaba da sauka don yan Najeriya su samu damar siya.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng