An karrama gwamnan Sokoto da lambar girmamawa ta fannin kimiyyar siyasa (Hotuna)
- Jami'ar Amurika ta Maryam Abacha wadda ke a jihar Maradi ta kasar Nijar ta karrama gwamnan jihar Sokoto da lambar girmamawa
- Jami'ar ta karrama gwamnan ne a lokacin da take bikin yaye dalibbanta wadanda suka kammala digirin farko da kuma na biyu fannoni daban-daban
Jami'ar Amurika ta Maryam Abacha (Maryam Abacha American University of Niger) wadda ke a jihar Maradi ta kasar Niger, a ranar Asabar, 8 ga watan Afrilu 2017 ta karrama gwamnan jihar Sokoto Honarabul Aminu Waziri Tambuwal (Mutawallen Sokoto) da lambar girmamawa ta fannin kimiyyar siyasa.
Jami'ar ta karrama gwamnan ne a lokacin da take bikin yaye dalibbanta wadanda suka kammala digirin farko su 300, a fannoni daban-daban, sai kuma wasu dalibai sama da dari wadanda suka kammala digirin su na biyu a fannoni da dama. Legit.ng
Daga cikin mahalarta taron sun hada da, tsohon gwamnan jihar Sokoto Dokta Aliyu Magatakarda Wamakko (Sarkin Yakin Daular Usmaniyya), gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, Babban sakataren gwamnatin jihar Sokoto, Farfesa Bashar Garba, kwamishinan kananan hukumomi da ci gaban al'umma ta jihar Sokoto, Honarabul Muhammad Manir Dan'iya.
KU KARANTA KUMA: A kama duk wani Gwamnan da yayi sata Inji Sanata Bukar Abba
Tawagar ta kuma hada da babban sakataren Ma'aikatar kula da kananan hukumomi ta jihar Sokoto, Alhaji Haruna Ahmad Tambuwal, kwamishinan Ilmi mai zurfi na jihar Sokoto, Alhaji Sahabi Isah Gada, tsohon sakataren jihar Sokoto, Alhaji Muhammad Maigari Dingyadi tare da sauran wasu manya manyan jami'un gwamnatin jihar Sokoto.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon da wani dan jam'iyyar APC ke bayyana nadamar kasancewa a cikin jam'iyyar
saboda masaloli daban-daban da ta ke fuskanta a hannun 'yan jam'iyyar
Asali: Legit.ng