Gaskiya ya bayyana! Ahmed Musa yayi fada da matarsa ne kan shirin sa na auren wata budurwa mai suna Juliet
- An rahoto cewa jarumin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Ahmed Musa na shirin auren mata ta biyu
- An bayyana cewa shawarar da ya yanke ne ya haddasa sabani tsakaninsa da matar sa Jamila a Landan
- Yazo cewa Musa na soyayya da wata budurwa mai suna Juliet tsawon shekaru biyu da suka wuce.
Rahotanni sun kawo cewa jarumin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Ahmed Musa na shirin auren mata ta biyu wanda ake zargin shine sanadiyan haddasa fada tsakanin jarumin da matarsa Jamila a birnin Landan.
A cikin daren ranar Laraba, 5 ga watan Afrilu ne yan sanda suka kama tsohon dan kungiyar na Kano Pillar, bayan sun samu kiran rikicin cikin gida a katafaren gidansa mai dakuna biyar dake Countesthorpe.
KU KARANTA KUMA: An kama Ahmed Musa a kasar Ingila saboda ya doki matar saAn kama Ahmed Musa a kasar Ingila saboda ya doki matar sa
Legit.ng ta jiyo cewan Ahmed Musa na shirin kara mata ta biyu ne mai suna Juliet sannan Jamila uwar ‘ya’yan Ahmed Musa guda biyu ta dunga ihu kafin daga bisani makwabta suka sanar da jami’an yan sanda.
A cewar rahoton, Musa da Juliet sun kasance suna soyayya tsawon shekaru biyu sannan kuma sunyi baiko a ranar Lahadi, 25 ga watan Maris, 2017.
An kuma kawo cewa Musa ya siya ma Juliet gida a unguwar masu kudi dake Lekki a jihar Lagas sannan kuma ya siya bata mota kirar Mercedes Benz C300.
A halin da ake ciki, ba’a sani ba ko Ahmed Musa da matar sa Jamila sun fara shirin rabuwa da juna.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng