Da kyau: Malaman Najeriya sun shiga tarihi a Duniya
– Malaman Jami’ar Bayero ta Kano sun shiga cikin littafan tarihi
– An jero Malaman Jami’ar cikin wadanda su ka fi kowa bincike a Duniya
– Da alamu Jami’ar na nema ta ciri tuta a Afrika da ma Duniya
Legit.ng ta samu labarin cewa wasu Malamai daga Jami’ar Bayero ta Kano sun shiga sahun Malaman da su ka fi kowa nazari da bincike a Duniya a halin yanzu. Wannan dai ba karamin abu ba ne musamman a wannan yanki na Duniya.
Malaman da su ka yi fice sune:
1. Farfesa Mahmud Umar Sani
2. Farfesa Muhammad Ajiya
3. Dr. Nuraddeen Magaji
4. Farfesa Yusuf M. Adamu
5. Dr. Ahmed A. Maiyaki
6. Dr. Umar Ibrahim Gaya
7. Dr. Dahiru Sani Shu’aibu
8. Dr. Muhammadu Yusuf Waziri
9. Farfesa Bashir Ali
10. Dr. Muhammad Shu’aibu Abubakar
KU KARANTA: Malamai za su shiga yajin aiki
Malaman da su ka yi fice a fannoni irin su lissafi, ilmin sinadarai, bangaren fasaha da sauran su sun shigo cikin sahun wadanda su ka fi kowa nazari a bana wanda a Afrika Najeriya na cikin wadanda aka dauka. Mun samu wannan bayani ne daga wata Mujallar Jami’ar.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga wata mata ita kuma da inda tayi fice
Asali: Legit.ng