An haramta wa Fulani gudanar da bukukuwan aure a cikin dare a garin Jeke, jihar Jigawa

An haramta wa Fulani gudanar da bukukuwan aure a cikin dare a garin Jeke, jihar Jigawa

Dakacin garin Jeke da ke a karamar hukumar Sule Tankarkar cikin Jihar Jigawa, Alhaji Alasan, ya kafa dokar hana Fulanin yankin sa gudanar da bukukuwan aure da sauran shagulgulan al’adu a cikin dare.

An haramta wa Fulani gudanar da bukukuwan aure a cikin dare a garin Jeke, jihar Jigawa
Dakacin garin Jeke ya haramta wa Fulani gudanar da bukukuwan aure a cikin dare

Jami’in yada labarai na karamar hukumar ne, mai suna Daudu Sulaiman, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a ranar Talata, 4 ga watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Rahama Sadau ta ƙaro wulaƙanci: Kalli wasu kyawawan Hotunan ta

Jami’in ya ce hakimin wanda kuma shi ne Dan Isan Gumel, ya bayar da wannan umarni ne yayin wani taro da ya yi tare da dakatai da masu unguwannin yankin sa.

Ya ce ya hana gudanar da bukukuwan ne domin kawo karshen yawan fadace-fadacen da ake yi a lokuttan bukukuwan. Hakimin ya ce sau da yawa irin wadannan fadace-fadacen kan haifar da asarar ruyuka da barnatar da dukiyoyi.

Har ila yau kuma, Hakimin ya yi kira ga jama’a da su guji halartar irin wadannan bukukuwa da kuma zuwa kasuwanni dauke da makamai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wasu jami'an gwamnati ne a kotu suna bada ba'asi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng