Muhimman abubuwa 21 da shirin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa ya ƙunsa wanda Buhari zai ƙaddamar a yau

Muhimman abubuwa 21 da shirin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa ya ƙunsa wanda Buhari zai ƙaddamar a yau

A yau Laraba 5 ga watan Afrilu ne ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da shirin gwamnatin tarayya na farfado da komadar tattalin arzikin kasa da akayi ma lakabi da suna, ERGP (wato economic recovery and growth plan) a birnin Abuja.

Muhimman abubuwa 21 da shirin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa ya ƙunsa wanda Buhari zai ƙaddamar a yau
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Kaakakin shugaban kasa Femi Adesina ya bayyana cewar shirin ERGP, wani tsari ne da gwamnati ta kirkiro don tabbatar da daurewar nasarorin data fara samu a fannin yaki da cin hanci, ingantsa tsaro da kuma farfado da tattalin arziki.

KU KARANTA: Mashawarcin shugaba Buhari ya ɗau alwashin maka Saraki a kotu, me yayi zafi? (Karanta)

Jaridar Premium Times ta bayyana cewar shirin ERGP zai taimaka wajen samar da cigaba ingantacce a kowanne fanni, gina al’ummar kasa da kuma samar da gasa a sha’anin tattalin arziki tsakanin kamfanunuwa masu zaman kansu.

Ga wasu muhimman abubuwa guda 21 da shirin ERGP ya kunsa da Legit.ng ta kawo muku.

1. Manufar ERGP shine farfado da tattalina arzikin kasa, gina al’umman kasa tare da samar da ingantaccen yanayi ma yan kasuwa.

2. Zai kara yawan kudade a hannun yan kasa da kashi 2.19 a shekarar 2017, da kuma kashi 7 a karshen 2020.

3. Zai rage karyewar darajan naira, tare da kara yawan kudaden shigar gwamnati daga Naira triliyan 2.7 zuwa naira triliyan 4.7 a karshen 2020.

4. Zai mayar da hankali kan tallafa ma kasuwanci tare da samar da tsare tsaren sabunta tattalin arzikin kasa wadanda za’ayi aiki da su a tsakanin shekarun 2017 zuwa 2020.

5. Ya mayar da hankali kan habbaka tattalin arzikin kasa tare da daidaita shi, karkatar da akalar tattalin arzikin kasa, tafiyar da mulki da samar da tsaro.

6. Kari ne kan tsari na gajeren zango da gwamnati ta fitar daya shafi kasafin kudin 2016 don samar ingantaccen cigaba a kasa zuwa shekarun 2017 da 2020.

7. Yana dauke da hanyoyin magance cin hanci da rashawa, inganta tsaro da sake gina tattalin arziki.

8. Manufarsu daya da tsarin majalisar dinkin duniya na cigaba da muradun karni.

9. Bambancinsu da sauran tsare tsare na baya, shine akwai niyya mai kyau tattare da shugaban kasa na ganin an gudanar da wannan tsarin.

10. An samar da sashin kula da tabbatar da isar da duk manufar da aka sanya a gaba a fadar shugaban kasa don tabbatar da ana gudanar da tsarin yadda ya kamata.

11. Yana dauke da tsarin kara yawan gangar mai da kasar ke fitarwa daga ganga miliyan 2.2 a duka rana zuwa ganga miliyan 2.5, tare da hanyar habbaka matatun man kasar don rage yawan man fetur din da aka siyowa daga kasar waje da kashi 60 a shekarar 2018.

12. Cigaba ne da tsarin nan na samar da cigaba a kasa ta hanyar samar da kamfanunuwa da kuma tsarin samar da kayayyan more rayuwa hannu da hannu.

13. Zai inganta dangantaka tsakanin gwamnatin tarayya, na jihohi da na kananan hukumomi don samun nasarar manufofin da aka sanya a gaba.

14. Tsarin ya jadda manufar samun alaka maimkyau tsakanin gwamnati da yan kasuwa masu zaman kansu don tabbatar da shirin karkatar da akalar tattalin arziki zuwa wasu fannoni da suka danganc noman da tsaro.

15. Ya lura da yadda za’a warware duk wasu matsaloli da suka daibaibaye tattalin arzikin kasa musamman ta hanyar amfani da yan kasuwa masu zaman kansu.

16. Ya samar da wasu muhimman hanyoyin farfado da tattalin arziki: samar da daidaito ga kananan yan kasuwa, samar da isashshen abinci da habba noma, tabbatar da isashshen mai da wutan lantarki, inganta sha’anin sufuri da kuma inganta tattalin arziki ta hanyar tayar da kananan masana’antu.

17. Akwai tsarin farfado da tattalin arziki cikin kankanin lokaci da kuma dabarun tabbatar da cigaba a dogon zango.

18. Ya hade ma’aikatan kasafin kudi da na tsare tsare don samun saukin gudanar da shirye shiryensa.

19. Yana dauke da tsarin kara yawan kudin shiga daga man fetur daga biliyan 700 a shekarar 2016 zuwa triliyan 1.3 a shekarar 2017, da kuma triliyan 1.45 a shekarar 2020.

20. Yana dauke da hanyoyin kara yawan gangan mai da muke fitarwa daga ganga miliyan 1.4 zuwa miliyan 2.2 a shekarar 2017, har ma zuwa ganga miliyan 2.5 a kasrhen shekarar 2020.

21. Zai taimaka ma gwamnatin samun rarar naira biliyan 50 a duk shekara ta hanyar rage mata kudaden da take kashewa da kashi 25.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kana danasanin zaban shugaba Buhari? kalli wannan bidiyon:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng