Waƙar siyasa ta shigar da Sadiq Zazzabi tsaka mai wuya
Fitaccen mawakin nan dan jihar Kano Sadiq Zazzabi ya shiga tsaka mai wuya biyo waya wata wakar siyasa da yayi mai suna maza bayan ka.
Sai dai wannan waka da Zazzabi yayi ya sanya shi zamowa naman farauta ga daya daga cikin bangarorinn siyasar Kano, da kuma hukumar tace fina finan jihar Kano wanda ke da hakkin tace fina finai ko wakoki kafin a shigar dasu kasuwanni don dacewa da ala’adun hausa da addinin musulunci.
KU KARANTA: Fashola ya lashe kyautan gwarzon minista a Najeriya
An gurfanar da Zazzabi gaban kuliya manta sabo inda ake tuhumarsa da aikata laifuka guda 2, na daya; sanya matan banza a cikin bidiyon suna rawar banza. Sai dai Zazzabi yace ana yi mai bita da kulli ne kawai sakamakon wakar da yayi mai suna ‘Maza bayanka’ ta nuna goyon bayansa ga Sanata Rabiu Kwankwaso, tare da sukar gwamnatin gwamna Ganduje.
“An kama ni kawai saboda goyon bayana ga Kwanwkaso,” inji shi.
Sai dai gwamantin Ganduje ta musanta zargin da Zazzabi ke yi mata. Idan ba’a manta ba dai Kwankwaso yayi mulkin Kano a shekarar 1999 zuwa 2003, sai ya kara daga 2011 zuwa 2015 duk tare da Gwamna Abdullahi Ganduje a matsayin mataimakinsa, a tsakankanin shekarun yayi ministan tsaro a gwamnatin Obasanjo.
Amma sai gashi yanzu da shi da tsohon mataimakin nasa Ganduje ba’a ga maciji, sakamakon har yanzu akwai jita jitan Kwankwaso na shinhsinan takarar shugabancin kasar nan duk da ya sha kayi a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na fitar da dan takarar shugaban kasa a shekarar 2015.
A wani kaulin kuma, kamar yadda Legit.ng ta binciko, Zazzabi na da tarin masoya a jihar Kano sakamakon wakokinsa da kuma shahara da yayi a matsayin mai goyon bayan Kwankwaso, don haka kama shi da aka yi yayi nuni da da cewa gwamnati ce ta kama shi, sai dai shugaban hukumar tace fina finai Ismail Afakallahu yace karya ne.
Dafifin jama’a ne suka garzaya kotu a ranar sauraron karar Zazzabi, dukkaninsu sanye da jar hula da fararen kaya, alamar kwankwasiyya kenan. A yayin zaman kotun, alkali maishari’a sai daya kore su daga kotu don ya yanke hukuncinsa amma suka ki fita. Ganin haka Alkalin ya bada belin Zazzabi.
A shekarar 2002 ne aka kafa hukumar tace finafinai don lura da wakoki ko fina finan da ake a yi a masana’antar Kannywood, wanda bincike ya gano har a kasashen yammacin Afirka ana kallonsu domin su dace da al’adar hausa da shari’ar muslunci. Wajibi ne sai an tantance fim ko waka kafin a fitar da shi kasuwa.
An sha fama da rikice rikice tsakanin yan Fim da hukumar sakamakon yan Fim da dama sun sha yin karantsaye ga dokar hukumar saboda yawan fitar da waka ko fim ba dake dauke da batsa ko makamancin haka ba tare da hukumar ta tantance su ba.
Ko a shekarar data gabata sai da aka sace wani mawaki mai suna Dahiru Daukaka a jihar Adamawa bayan yayi wata waka dake sukar gwamnatin jihar, amma daga bisani an sako shi. Ana ganin irin matsalar da Zazzabi ke fuskanta kenan, sai dai masana siyasa suna has ashen kaikayi zai koma kan mashekiya fa, tun da dai jama’a na zargin an kama shi ne saboda siyasa.
‘Ko dai siyasa ne ta sa aka kama shi, ko ba siyasa bane, za’a cigaba da kallon kamen da aka yi ma Zazzabi a matsayin cin dudduniya saboda banbancin siyasa, musamman alakarsa da Kwankwasiyya,” inji Adamu Musa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Shina kana daba sanin zaben shugaba Buhari a shekarar 2015?
Asali: Legit.ng