Abin al-ajabi: Wani yaro mai shekara 20 ya yanka Uwarsa

Abin al-ajabi: Wani yaro mai shekara 20 ya yanka Uwarsa

Wani mummunan al’amari da ta faru a karamar hukumar Umuchagu Osokwa a birnin Osisioma Ngwa a jihar Abia ta jefa al’umman hukumar cikin bakin ciki da kunci a yayin da wani matashi dan shekara 20 ya yanka uwarsa.

A cewar jaridar Vanuard, al'amari ya faru ne a yammacin Alhamis, da misalin karfe 6.30 a yayin da wannan mata mai suna Cecilia Nwanjie ta dawo daga gona, ta tarar da danta wanda ke wata uwa duniya ya iso gidan, Cecilia cike da annashuwa suka gaisa sai ta nufi madafi domin daura abinci.

KU KARANTA KUMA: An maka Bukola Saraki da wasu Sanatoci a KotuAn maka Bukola Saraki da wasu Sanatoci a Kotu

Yaron nan na biye biye da uwarsa har sai da ya tabbatar gidan babu kowa, ya nufe ta da adda, ya murkushe ta sai ya datsa mata a wuya, kara da ihun cecilia yasa jama’ar unguwan suka nufo wannan gida amma tuni yaron ya tsere da jinin uwar da ya tatsa.

Legit.ng ta samu labarin cewa, wasu daga cikin ‘yan unguwar sunga shigowar wannan yaro, shi yasa suka ce lallai shi ya aikata wannan danyen aiki.

Mazauna unguwar sun bayyanawa manema labarai cewa Cecilia tun bayan mutuwar mijinta ne take ta fadi tashi don ganin cewa ta ciyar da kanta, tana zaune ita kadai ne a yayin da yayanta biyu suna zaune a wata uwa duniyan ne basu damu da ita ba.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa na kara sukurkucewa Dino Melaye

Jami’ai tsaro sun cigaba da bincike da neman wannan ‘da ruwa a jallo amma har izuwa yanzu ba a ga yaron nan ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ma'aikata sun yi zanga-zanga a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel