Kungiyar Izala za ta bude makarantar alkalai da limamai a Jos

Kungiyar Izala za ta bude makarantar alkalai da limamai a Jos

Kungiyar Izala ta kammala shirin bude wata sabuwar makarantar alkalai da limamai a garin Jos babban birnin jihar Filato a watan nan ta Afrilu.

Kungiyar Izala za ta bude makarantar alkalai da limamai a Jos
Shugabanin kungiyar Jama'atu Izalatil bid'atu wa ikamati sunnah a lokacin ziyarar aikin makarantar alkalai da limamai a Jos babban birnin jihar Flato

Kungiyar Jama'atu Izalatil bid'atu wa ikamati sunnah mai hedikwata a Jos babban birnin jihar Flato, karkashin jagorancin shugaban majalisar malamai ta kasa, Assheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, tana sanar da bude makarantar alkalai da limamai, ladanai da shugabanni da kuma 'yan agaji. Shugaban na mai cewa, insha Allahu a ranar Litini, 10 ga watan Afrilu 2017 za a bude makarantar, kuma za a fara karatun ne a wannan rana ta Litinin.

KU KARANTA KUMA: Yawancin almajiran Kano sun fito ne daga Chadi da Nijar

Shugaban ya kara da cewa za a kuma fara rijistar dalibai ne tun ranar Asabar, 8 ga watan Afrilu a harabar makarantar dake sarkin Mangu cikin garin Jos.

Legit.ng ta samu wannan sanarwa ne daga bakin shugaban makarantar alkalai ta kasa, Hafiz Aminu Yusuf Nuhu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda sunan Allah ya bayyana a jikin itacen moringa

Asali: Legit.ng

Online view pixel